AhlolBayt News Agency (ABNA)

source : parstoday
Cumartesi

11 Temmuz 2020

11:09:19
1054361

Masu Zanga-zanga A Kasar Mali Sun Kutsa Cikin Gidan Radiyo Da Talbijin Da Kuma Majalisar Dokokin Kasar

“Yan jarida da su ke bin diddigin abubuwan da su ke faruwa a cikin kasar ta Mali, sun ce an killace wani yanki mai muhimmanci a birnin Bamako da a nan ne mafi yawancin ofisoshin gwamnati suke.

Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Majiyar ‘yan jaridar kasar ta Mali ta ce wani sashe na masu Zanga-zangar sun kunna wuta a wani sashe na ginin majalisar dokokin kasar tare da lalata shi, kuma mutum guda ya rasa ransa.

Har ila yau masu Zanga-zangar sun kutsa cikin ginin Radio da talabijin din kasar a birnin Bamako da hakan yayin sanadiyyar dakatar da watsa shirye-shirye.

Al’ummar kasar Mali suna yi Zanga-zanga ne a matsayin matsin lamba ga gwamnatin shugaba Boubakar Kaita da ta yi sauye-sauye a bangarori daban-daban na harkokin yau da kullum na raywuar al’ummar kasar.

342/