5 Mayıs 2020 - 08:06
Nasrallah : Babu Wasu Harkoki Da Hezbollah Ta Ke Gudanarwa A Jamus

Shugaban kungiyar Hezbollah, ta kasar Labanon, Hassan Nasrallah, ya ce babu wasu harkoki da kungiyar ta ke gudanarwa a kasar Jamus, kwanaki kadan bayan da gwamnatin kasar ta Jamus ta haramta kungiyar a kasar.

(ABNA24.com) Shugaban kungiyar Hezbollah, ta kasar Labanon, Hassan Nasrallah, ya ce babu wasu harkoki da kungiyar ta ke gudanarwa a kasar Jamus, kwanaki kadan bayan da gwamnatin kasar ta Jamus ta haramta kungiyar a kasar.

Sayyid Hassan Nasrollah, ya ce dama mun sha fadar cewa bamu da wasu harkoki da muke gudanarwa a kasar Jamus, kuma wannan batu haka yake dari bisa dari.

Matakin da gwamnatin Jamus ta dauka a cewarsa, siyasa ce, ta mika kai ga Amurka da kuma birge Isr’aila.

A ranar Alhamis data gabata ce ma’aikatar cikin gidan kasar Jamus, ta sanar da cewa ta haramta gabadayen ayyukan kungiyar ta Hezbollah ke gudanarwa a kasar.



/129