(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iran ta bayar da sanarwar cewa za ta fara sayar wa kasashen Jamus da Turkiya kayakin gwajin cutar Corona ko (test kits) bayan da ta sami izinin ma’aikatar kiwon lafiyan kasar na saida su ga masu bukata a kasashen waje.
Sourena Sattari mataimakin shugaban kasa a bangaren bunkasa ilmin kimiya da kere-kere na kasar ta Iran, ya fada wa kamfanin dillancin labaran “IRNA” na kasar cewa kasar ta wadatu da wadannan kayakin aikin gwajin cutar Corona bayan yaduwar cutar Corona a kasar a farkon wannan shekara.
Ya zuwa yanzu dai cutar Corona ta kashe mutane 248,300 a duk fadin duniya, 6,200 daga cikinsu ‘yan kasar Iran ne. Cutar ta bulla ne da farko a birnin Wuhan na kasar China a karshen shekarar da ta gabata, sannan ta yadu da sauri zuwa kasashen duniya.
Kasar Iran na daga cikin kasashen da cutar ta fara yaduwa cikinta bayan kasar China.
/129
5 Mayıs 2020 - 08:06
News ID: 1033663
Gwamnatin kasar Iran ta bayar da sanarwar cewa za ta fara sayar wa kasashen Jamus da Turkiya kayakin gwajin cutar Corona ko (test kits) bayan da ta sami izinin ma’aikatar kiwon lafiyan kasar na saida su ga masu bukata a kasashen waje.